Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Sayyida Fatima al-Zahra (a.s)...Tsarkakka

Hakika hadisan Manzon Allah (s.a.w.a) a kan Fatima da mijinta da 'ya'yanta, sun kasance maimaita zantukan wahayi ne, kuma bayani ne na abin da Alkur'ani ya kunsa, wanda ya tabbatar musu da tsarki da daukakar matsayi. A kansu Allah Ya saukar da bayyanannun ayoyi da ya kebance su da su, kamar su Ayar Tsarkakewa, Ayar Mubahala, Ayar Kauna, Surar Insan(1). da wasunsu na daga ayoyin Alkur'ani mai girma.

Malaman ruwaya da tafsiri sun ruwaito fadar Allah Madaukaki: "Lallai Allah na nufin kawar da kazanta ne daga gare ku Ahlulbaiti Ya kuma tsarkake ku tsarkakewa" da cewa ta sauka ne a kan Ali, Fatima Hasan da Husaini (a.s.).

Daga cikin su akwai abin da Ummu Salama matar Manzon Allah (s.a.w.a) ta ruwaito, inda ta ce: "Fatima ta zo wajen Manzon Allah (s.a.w.a) da wani akushi mai dauke da abinci a cikinsa, sai ta aje a gabansa. Sai Manzo ya ce: "Ina baffanki da 'ya'yanki biyu?" sai ta ce: "Suna gida"Sai Manzo ya ce: "Kira su." Sai Fatima ta tafi ta sami Ali (a.s.) ta ce masa: "Manzo na kiranka da 'ya'yanka biyu" Sai Ummu Salama ta ci gaba da cewa:"Yayin da Manzo ya gan su suna zuwa sai ya mika hannunsa a kan wani mayafi da ke wajen barci, sai ya jawo shi ya shimfida shi, sai ya zaunar da su a kansa, sannan ya kama geffan mayafin hudu da hannun damansa ya rufe da shi, sannan ya daga hannunsa na dama sama ya yi addu'a da cewa: "Ya Allah! Wadannan ne Ahlulbaitina, to ka kawar musu da duk wata dauda ka kuma tsarkake su tsarkakewa(2)".

Manzo (s.a.w.a) ya so ya kara bayyana ko su wane ne Ahlulubaitinsa, haka nan kuma don ya dada fayyace ma'anar ayar sai ya rika bi ta gidan Fatima da Ali da Hasan da Husaini har na tsawon watanni shida, duk lokacin da zai fita zuwa salla, sai ya tsaya a daidai kofarsu yana maimaita wannan aya mai albarka(3)".

Dangane da Ayar Mubahala kuwa da Allah ke cewa:

"To, wanda ya yi musu da kai a cikinsa, a bayan abin da ya zo maka daga ilmi, to ka ce: "Ku zo mu kirayi 'ya'yanmu da 'ya'yanku da matanmu da matanku da kanmu da kanku, sa'an nan kuma mu kankantar da kai, sa'an nan kuma mu sanya la'anar Allah a kan makaryata". (Surar Ali Imrana, 3: 61)

Malumman tafsiri sun dace a kan cewa wadanda ake nufi da 'ya'yanmu a wannan aya su ne Hasan da Husaini, "matanmu"kuma na nufin Fatima, kuma mu kanmu na nufin Ali, kuma da su Manzon Allah (s.a.w.a) ya fita zuwa Mubahala.

Wannan kadan ne daga tarin abin da ya sauka a kansu, mun ambaci dan abin da ya dace da wannan matsayin ne.



____________
1- Ayar Tsarkakewa (Suratul Ahzab: 33:33), Ayar Mubahala, (Suratu أli Imran: 3:61); Ayar kauna kuma na (Suratush Shura: 23).

2- Takiyyuddin Ahmad bin Ali al-Makrizi, a cikin Fadhlu Ahlulbait, bugu na 2, shafi na 25; daga Tafsirin Dabari, juzu'i na 22, shafi na 7; da Dabari, cikin Zakha'irul-Ukbah, shafi na 21.

3- Al-Makrizi, Fadhlu Ahlul-bait, bugu na 2, shafi na 24; da Dabari, cikin Zakha'irul-Ukbah, shafi na 24; haka nan Ahmad da Tirmiz sun ruwaito shi.

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din


Insane